A ranar Litinin ne Alhaji Suleiman Othman Hunkuyi ya karbi tikitin takarar gwamnan jihar Kaduna na zaben fidda gwani na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) bayan ya samu ƙuri’u 732.
A yanzu dan takarar na NNPP zai kara da Isa Mohammed Ashiru na jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), Sanata Uba Sani na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), da sauran ‘yan takarar gwamna na wasu jam’iyyun siyasa a babban zabe na 2023.
Hunkuyi ya wakilci mazabar Kaduna ta Arewa a majalisar dattawan kasar, a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kafin ya koma PDP a 2019.
Tsohon dan majalisar dai ya fice daga PDP ne a watan Fabrairun 2022 ya koma NNPP.
Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Bello Ma’aji wanda ya bayyana takarar Hunkuyi a karkashin jam’iyyar NNPP, ya ce daga cikin wakilai 765, wakilai 732 ne suka amince da su, wadanda suka wakilci adadin da ake bukata na zaben fidda gwani.