fidelitybank

Hungary ta tura sojoji don yakar ‘yan ta’addan Chadi

Date:

Majalisar dokokin Hungary ta amince da tura sojoji 200 zuwa ƙasar Chadi, domin inganta zaman lafiya da tsaro, da kuma yaƙi da ta’addanci.

Chadi, ƙasar da ke tsakiyar Afrika na fuskantar barazanar tsaro daga ƙungiyoyin masu aikata laifi.

A cewar ma’aikatar tsaron kasar, tura dakaru daga farkon 2024 zuwa Disamban 2025, zai kuma rage matsin lamba na kwararar bakin haure zuwa Turai.

A halin da ake ciki, majalisar ministocin kasar Chadi ranar Laraba, ta amince da wata doka da za ta yi afuwa ga mutanen da ke da hannu a zanga-zangar adawa da gwamnati ranar 20 ga Oktoban 2022.

Mutane akalla 50 ne suka mutu lokacin da ɗaruruwan masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Chadi suka yi arangama da jami’an tsaro.

Masu zanga-zangar dai na adawa ne da tsawaita wa’adin gwamnatin riƙon kwarya da shekaru biyu, inda suka zargi shugaban rikon kwaryar Janar Mahamat Idris Deby da neman ci gaba da zaman dafa’an a kan karagar mulki.

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp