fidelitybank

Hungary ta ce ba za ta taimakawa Ukraine ba a fadan Rasha

Date:

Firaministan Hungary Viktor Orban, ya yi watsi da buƙatar Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky na neman ƙasar ta ba su makamai da kuma saka wa Rasha tsauraran takunkumai, yana mai cewa “hakan ya saɓa wa muradun Hungary”.

Orban ya ƙi amincewa da buƙatar ta Zelensky a wurin taron Majalisar Turai “saboda sun saɓa wa muradun Hungary”, a cewar wani magana da yawun gwamnatin Hungary cikin wata sanarwa.

“Hungary ba ta son ta goyi bayan wani ɓangare a yaƙin nan, saboda haka ba za ta bari a kai makamai Ukraine ba,” in ji Kovacs.

Orban ya ce ‘yan asalin Hungary da ke zaune a yammacin Ukraine za su shiga cikin zullumi idan ƙasarsu ta kai wa Ukraine ɗin makamai.

Hungary wadda mamba ce a ƙawancen tsaro na Nato, ta ƙi aika wa Ukraine makamai da kuma ƙyale ta ta bi sararin samaniyarta. Sai dai ta bar rabin miliyan na ‘yan Ukraine sun shiga ƙasarta.

Orban ɗan jam’iyyar kishin ƙasa, ya ƙulla ƙawance da Shugaban Rasha Vladimir Putin a ‘yan shekarun nan.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp