fidelitybank

Hukuncin Kotu: Magoya baya ku kwantar da hankalin ku mu na nazari a kai

Date:

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, ya yi kira ga magoya bayansa a jam’iyyar APC mai mulki a jihar da su kwantar da hankalinsu, su kuma bi hanyar zaman lafiya da bin doka da oda.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a matsayin martani ga hukuncin da wata babbar kotun Abuja ta yanke ranar Juma’a, wanda ya nuna goyon bayan wani bangare na jam’iyyar a jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar, wadda PlatinumPost ta samu a ranar Juma’a, gwamnan ya ce” Tunda lamarin na cikin jam’iyya ne, gwamnati da jam’iyyar APC a halin yanzu muna nazari kan lamarin, domin samun mafita”.

Gwamna Ganduje ya kuma umurci jami’an tsaro da kada su lamunci rashin bin doka da oda, domin gwamnati ba za ta amince da duk wani aika-aika da ta’addanci ko tashin hankali a wani yanki na jihar ba, da sunan siyasa ko wani fage.

Sanarwar ta kuma nuna godiya ga ‘yan jam’iyyar a dukkan matakai da sauran masu ruwa da tsaki bisa jajircewar da su ka nuna wajen marawa jam’iyyar baya.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Sudan ta Kudu ta yi ta’aziyyar Buhari

Mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Sudan ta Kudu, Ambasada Akuei...

Trump ya na fama da cuta mai kumbura kafa da toshewar hanyar jini

A ranar Alhamis ne Fadar White House ta sanar...

Yadda aka gudanar da addu’o’in Buhari a Villa

A ranar Alhamis ne aka gudanar da addu'o'i ga...

Rasha tarnaki ce a wajen Tarayyar Turai – Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya shaidawa BBC cewa...

Amurka ba ta goyon bayan Isra’ila a harin Syria – Trump

Amurka ta ce ba ta goyon bayan hare-haren da...

Tinubu zai zo Kano ta’aziyyar Dantata

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu zai kai ziyara Kano yau...

Tarayyar Turai tamince da ƙaƙaba wa Rasha sabbin takunkumai

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da ƙaƙaba wa Rasha...

Gwamnan Filato ya zargi Jami’ai da kin kama ‘yan bindiga

Gwamnatin jihar Filato ta zargi jami'an sojojin ƙasar da...

Za a yi wa Buhari addu’a a Abuja

Gwamnatin Tarayya za ta jagoranci gudanar da taron addu'o'i...

Buhari ya ban umarni na kula da Talakawan Najeriya – Peter Obi

Jagorar jam'iyyar LP a Najeriya, Peter Obi ya ce,...

Sojojin hadin gwiwa sun hallaka ‘yan Boko Haram a tafkin Chadi

Rundunar hadin gwiwa mai yaƙi da Boko Haram a...

Na yi rashin aboki na gari kuma Najeriya ta rasa mutumin kirki – Tinubu

Shugaban Kasa, Bola Tinubu, na ci gaba da alhinin...
X whatsapp