Gwamna Bello Mohammed na jihar Zamfara ya ce, hukuncin da Kotun Koli ta yi kan karɓar tsofaffin kuɗin naira da kuma bin hukuncin da Babban Bankin ƙasa CBN, ya yi nasara ce ga dukkanin ƴan Najeryia.
Gwamnan wanda shi da takwarorinsa na jihar Kaduna da Kogi suka fara shigar da ƙara kan wa’adin da Babban bankin ya sa na daina amfani da tsofaffin takardun kudin naira 200 da 500 da kuma 1,000 kafin wasu gwamnonin su mara musu baya a shari’ar,
ya ce a yanzu gaskiya ta yi halinta, duk da cewa a da ana zarginsu da cewa sun ɗauki matakin ne saboda zaɓen shugaban ƙasa, duk kuwa da cewa a zahiri take ƴan ƙasar na shan wuya saboda canjin.
Karanta Wannan: Sojoji da ‘Yan Banga sun dakile harin ‘yan bindiga a Zamfara
Ya kara da cewa a yanzu ƴan Najeriya za su samu sa’ida a kan wannan lamari, yana mai cewa suna fatan ganin an samar da ƙarin takardun kuɗi a tsakanin jama’a domin sauƙaƙa wahalar da ake ciki, yayin su kuma waɗanda suke da tsofaffin takardun ba za su yi asara ba.
Matawalle ya kuma yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari a kan yadda ya nesanta gwamnatinsa daga matakin Babban bankin na ƙin mutunta hukuncin Kotun Ƙoli na matsar da wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin na naira har zuwa ranar 31 ga watan Disamba na wannan shekara.
Tun a ranar 3 ga watan nan na Maris Kotun Ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin ɗaga wa’adin daina amfani da tsofaffin takardun kuɗin amma Babban Bankin ya yi shiru kan ambata cewa ya amince da hukuncin, wanda hakan ya sa jama’a suka shiga tsaka-mai-wuya, kan amfani da tsofaffin kuɗin.
Halin da jama’a suka shiga na ƙunci da sukar gwamnati da ake yi na ƙin magana kan lamarin wasu ke ganin ya tilasta wa fadar shugaban ƙasar a jiya Litinin ta fito ta nesanta kanta ga ƙin bin umarnin, abin da ya sa a yanzu Bankin ya fito ya bayar da kai.