fidelitybank

Hukumomi sun gaza wajen tabbatar da adalci a kan sojojin da suka jefa bam a Nasarawa – Kungiyar kare hakki

Date:

Shekara ɗaya bayan wani mummunan harin da jirgin saman sojin Najeriya ya kai a garin Rukubi na jihar Nasarawa da ya yi sanadin mutuwar mutane 40, waɗanda abin ya shafa da iyalansu har yanzu na jiran a yi musu adalci.

Shugaban ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi, ya ce hukumomin ƙasar sun gaza wajen tabbatar da adalci da kuma bin diddigin harin da aka kai.

Sanusi ya soki yadda ake amfani da hare-hare ta sama wajen tabbatar da doka da oda, yana mai cewa hakan ya saɓa wa doka, haramun ne da kuma yin amfani da karfi ne fiye da kima, yana mai jaddada cewa tamkar tsawaita rashin adalci ne ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

“Rashin hukunta sojojin da ke da alhakin kai irin wannan harin kan fararen hula na nuna rashin mutunta rayuwar ɗan’adam da kuma ƙara ƙarfafa gwiwar kai irin wannan harin nan gaba tare da kuma ƙara jefa mutanen da ke zaune a yankunan karkara, waɗanda ke fama da tashe-tashen hakula cikin hatsari mai girma.” in ji shi.

“Hare-haren jiragen sama tare da yawaitar kashe-kashen mutane ba bisa ƙa’ida ba sun zama daya daga cikin jerin manyan laifukan take haƙƙin bil’adama na baya-baya nan da sojojin Najeriya ke yi.”

“Dole ne mahukuntan Najeriya su bai wa sojoji umarni da su rika bai wa rayuwar fararen hula fifiko da muhimanci da kuma mutunta hakkin dan’adam a koda yaushe yayin gudanar da dukkan ayyukan tsaro. Dole ne gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta gudanar da bincike mai zaman kansa, ba tare da nuna son kai ba, kuma mai inganci, kan harin da aka kai wa Rukubi ta sama, da ma wasu da dama da suka haddasa kashe-kashe ba bisa ka’ida ba.

“Ya kamata a gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a gaban shari’a ta hanyar shari’a ta gaskiya, ciki har da wadanda ke da alhakin daidaikun mutane da na sojoji da manyan kwamandojin sojoji.”

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp