Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), a ranar Talata ta fitar da bayanan sunayen ‘yan takara a zaben gwamnan jihar Osun.
Hukumar a cikin wata sanarwa da kwamishinan kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kada kuri’a, Festus Okoye, ya fitar a Abuja, ya ce, an buga jerin sunayen ne a ofisoshin INEC na jihar da na kananan hukumomin jihar Osun kamar yadda doka ta tanada.
Okoye ya ce, an buga jerin sunayen ne bisa bin dokar zabe ta 2022, bayan da jam’iyyun siyasa suka miƙa sunayen ‘yan takara.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa, ‘yan takara 15 da aka buga, yayin da babu daya daga cikin ‘yan takarar gwamnan da bai amince ba, shida daga cikin mataimakan gwamna mata ne.
‘Yan takarar da aka buga sun hada da Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC , Adeleke Nurudeen na jam’iyyar PDP da Omigbodun Akinrinola na SDP.
Ya tunatar da jam’iyyun siyasa cewa, a karkashin sashe na 32(2) na dokar zabe ta 2022, duk jam’iyyar da ta lura cewa, sunan dan takararta ya bata a cikin jerin sunayen za ta sanar da Hukumar a rubuce.