Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya nada attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, da kawunsa, Aminu Dantata, da Abdulsamad Rabi’u a matsayin mambobin hukumar Zakka da Hubsi ta jihar.
Wannan ci gaban ya biyo bayan amincewar Majalisar Zartaswa ta Jihar Kano da ta sake kafa Hukumar Zakka da Hubsi ta Kano tare da Dokta Ibrahim Mu’azzam Maibushira a matsayin Shugaban Hukumar.
Sanarwar da Kwamishinan Yada Labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta kuma bayyana Dr AbdulMutallab Ahmed a matsayin kwamishinan I, Dr. Lawi Sheikh Atiq kwamishinan II na hukumar.