A ranar Alhamis din da ta gabata ne Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta fara raba wasu muhimman kayyakin zaben Gwamnan Jihar Ekiti da za a yi ranar Asabar.
An raba kayayyakin ne a ofishin INEC na jihar Ado Ekiti tare da halartar ‘yan jarida da jam’iyyun siyasa da jami’an tsaro ga ofisoshin zabe da ke fadin kananan hukumomi 16 na jihar.
Kwamishinan zabe na jihar, Dr Adeniran Tella, wanda ya raba kayan ya ce, jami’an zaben za su kai kayan zuwa kananan hukumominsu, inda za a tura su wuraren rajista (RACs), sannan kuma a rumfar zabe da safiyar Asabar.