Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Edo (EDSIEC), ta dakatar da gudanar da zaben kananan hukumomin da aka shirya gudanarwa a ranar 19 ga Afrilu, 2022.
A cewar wata sanarwa da Emmanuel Abebe ya sanya wa hannu a madadin shugaban hukumar ta EDSIEC, an dakatar da zaben ne, saboda umarnin da babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi wa hukumar.
EDSIEC ta ce, an dakatar da duk wasu matakai na gudanar da zabukan, har zuwa lokacin da za a saurari karar da kuma tantance kudirin.
Ya ce: “An sanar da jama’a ne, saboda abin da ya kunsa a cikin jaridar Vanguard ta ranar 7 ga Afrilu, 2022 wanda babbar kotun tarayya da ke Abuja ta hana EDSIEC gudanar da karamar hukumar zabuka a jihar da aka shirya yi a ranar 19 ga Afrilu, 2022, don haka an dakatar da duk wasu hanyoyin da za su kai ga gudanar da zaben, har sai an saurari karar da kuma tantance kudirin a kan sanarwa.”