fidelitybank

Hukumar ‘yan sanda ta dakatar da jami’ai 2 daga tawagar Abba Kyari

Date:

Hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da wasu jami’ai da ke tare da Abba Kyari a zargin harkallar kwayoyi da a ke yi musu.

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan, bayan da hukumar NDLEA ta sanar da neman Abba Kyari tare da kama shi da aka yi.

Abba Kyari da wasu mutum hudu ‘yan tawagarsa na kan zargin safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa, hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda ta dakatar da ACP Sunday Ubua da ASP James Bawa daga aiki daga ranar Litinin 14 ga Fabrairu, 2022.

Jami’an ‘yan sandan biyu na aiki ne a karkashin DCP Abba Kyari da aka dakatar a cikin tawagar leken asiri ta IRT ta rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Hukumar ta kuma umarci Sufeto Janar na ‘yan sanda da ya kuma lura cewa, DCP Abba Kyari, wanda kafin zargin NDLEA dama ya na kan dakatarwa, zai ci gaba da kasancewa har sai an kammala bincike. An bukaci Sufeto-Janar na ‘yan sandan da ya dakatar da Sufeto Simon Agrigba da Sufeto John Nuhu bisa ga ikon tawagar.

nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp