Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ce ba a fahimci maganarsu da suka yi ba ta batun sadaki a Kano.
Shugaban hukumar, Malam Abbas Abubakar Daneji, wanda ya yi wa manema labarai karin haske a ofishinsa ranar litinin 18 ga watan Augusta 2025, ya ce a taronsu na ranar Alhamis da ta gabata da hukumar zakka da Hubusi da kuma hukumar Hisba da sauran masu ruwa da tsaki, sun tsayar da matsaya akan abun da ya shafi Zakka da diyar rai da kuma sadakin aure a jihar Kano, wanda jama’a suka fahimci batun ba daidai ba musamman sadakin aure.
Sheikh Daneji, ya ce, da yawa daga cikin matasa, sun fi tsauwalawa wajen aure na hanasu yin aure ,hakan ya sa hukumar shari’a da sauran Malamai su ka zauna tare da duba halin kunci da ake ciki suka tsayar da cewa za a iya biyan naira dubu 20 a matsayin sadaki, sannan za’a iya biyan sama da haka.
A baya bayan nan an ta cece-kuce kan jita jitar da a ke yadawa cewa, hukumar shari’a ta Kano ta kayyade Naira dubu 20 a matsayin mafi sadakin Aure a Kano.