fidelitybank

Hukumar PCACC a Kano ta kama manjojin gidan mai da suka siyar fiye da kima

Date:

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano ta kama manajojin gidajen man fetur hudu, bisa zargin sayar da mai fiye da farashin da aka kayyade na Naira 165 kan kowace lita.

Hukumar ta kama ma’aikatan gidajen mai biyu kan lamarin, wanda a ka kama su ne bayan samun korafe-korafe daga jama’a cewa, duk da karancin man da ake fama da shi wasu gidajen mai na sayarwa kan Naira 200 zuwa Naira 208 a jihar Kano.

Hukumar da ke karbar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC), da shugaban ta Mahmoud Balarabe ke jawabi a wani taron manema labarai da ya gudana a ofishinsa a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu. Mukaddashin shugaban hukumar, Mahmoud Balarabe, ya ce, an kama mutanen ne a gidajen mai mabanbanta da ke cikin garin Kano.

Ya ce, “Daya mutumin kuma ma’aikacin mai ne, kuma mun kama shi ne bayan manajan na sa ya haura katanga ya gudu. Akwai gidan mai da muka gano cewa, sun riga sun siyar da lita 18,000 kan Naira 200, inda muka samu Naira 630,000 a kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba. An gano dayan gidan mai ya boye sama da lita 4,000. Mun tursasa su ci gaba da sayar wa mutane lita 4,000 da su ka boye.” A cewar Mahmoud in ji BBC.

spw news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp