fidelitybank

Hukumar NUPRC mai sa ido kan harkokin man fetur a cikin ruwa za ta sauya ofishin ta zuwa Legas

Date:

Hukumar NUPRC mai sa ido kan harkokin man fetur a cikin ruwa a Najeriya ta kammala shirye-shiryen sauya matsugunnin wasu ofisoshinta daga Abuja zuwa Legas.

Wannan da alama na zuwa ne bayan matakin baya-bayan nan na mayar da wasu ma’aikatan babban bankin Najeriya, CBN da sauya matsugunin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya – FAAN da wani sashe na babban bankin kasar, CBN.

Wasu ma’aikatan NUPRC sun tabbatar wa BBC cewa hukumar na shirye-shiryen É—aukan wannan matakin.

Matakin na mayar da wasu ma’aikatan CBN zuwa Legas da É—auke hukumar FAAN zuwa BIRNIN ya janyo cece-kuce inda masu ruwa da tsaki suka nuna rashin gamsuwarsu da matakin.

NUPRC da a baya ake kira DPR mai sa ido kan harkokin haÆ™owa da sayar da man fetur a Najeriya, sashe ne a Æ™arÆ™ashin ma’aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya.

Hukumar na lura da mai da iskar gas domin tabbatar da bin Æ™a’idoji da dokokin da suka dace da kuma lura da wasu dokoki da suka shafi fita da shigowa da albarkatun mai cikin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar, Gbenga Komolafe ya soma yunƙurin sauya matsugunin wasu ofishoshin hukumar daga Abuja.

To sai dai wani babban ma’aikaci a hukumar wanda ya zanta da BBC, ya musanta kalaman na shugaban hukumar.

“Ya yi iÆ™irarin rashin isasshen wuri ga sabbin ma’aikatan da yake son ya É—auka aiki. Wannan ba dalili ba ne kasancewar shekaru biyu da suka gabata ne aka É—auke ofishin daga Legas zuwa Abuja, sannan ana gab da Æ™arasa makeken ginin hedikwata.” In ji ma’aikacin.

Sabuwar hedikwatar gini ne mai hawa 10 da majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya ta amince da shi a 2020 wanda kuma aka tsara kammalawa cikin wata ashirin da huÉ—u.

spw

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp