Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama magunguna 203, 879 daban-daban da kuma wasu haramtattun abubuwa a samamen da suka kai a jihohin Abia, Kaduna, Yobe da Kogi.
Har ila yau, ta ce, ta dakile wani sabon yunkurin da kungiyoyin masu safarar miyagun kwayoyi ke yi na fitar da Tramadol, Ecstasy MDMA da Cannabis zuwa Milan, Italiya da Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa ta filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, MMIA, Ikeja Legas.
Kakakin ta, Femi Babafemi, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata, ya kuma ce an kama wasu ‘yan kungiyar 5 da ke aikin daukar aikin bogi a cikin jami’an tsaro a ayyukan hadin gwiwa a jihohin Zamfara, Kebbi da Bauchi.