A daidai lokacin da ake dakon fara ƙuri’a, shugaban hukumar tattara bayanan sirrin Amurka ya yi gargaɗin cewa wasu “ƙasashen waje” – ciki har da Rasha – na yunƙurin yin wasu “abubuwa da za ɓata nagartar zaɓen na Amurka, da jawo rabuwar kai a tsakanin ƴan Amurka.”
A wata sanarwa da ofishin darakta na hukumar tattara bayanan sirrin, da FBI da sauran hukuman leƙen asirin ƙasar, sun zargi ƙungiyoyi da suke da alaƙa da Rasha suna ƙoƙarin tayar da tarzoma da sake dawo da batun zargin maguɗin zaɓe.
Hukumomin sun bayyana a sanarwar cewa, “wasu ƙungiyoyi masu alaƙa da Rasha sun wallafa wasu rubuce-rubuce cewa jami’an zaɓe a wasu manyan jihohi suna ƙoƙarin yin maguɗi. Sanarwar ta kuma zargi Iran da zama “wata barazana” ga zaɓen na Amurka.
Tuni dai Rasha da Iran sun musanta waɗannan zarge-zarge