fidelitybank

Hukumar Kwastam ta dakatar da aikin sintiri na hadin gwiwa

Date:

Hukumar Kwastam ta sanar da dakatar da aikin sintirin haɗin gwiwar jami’an tsaro na bakin iyakokin ƙasar, wato Joint Border Patrol Team (JBPT).

Kakakin hukumar, Abdullahi Maiwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.

A ranar 11 ga Disamba ne majalisar wakilai ta ba kwamitinta na kwastam umarnin gudanar da bincike kan ayyukan jami’an kwastam a bakin iyakokin ƙasar bayan zarge-zargen almundahana da cin zarafin ƴanƙasar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Amma kakakin rundunar ya ce hukumar ta ɗauki wannan matakin ne a yunƙurinta na inganta tsaron bakin iyakokin domin fuskantar 2025.

Maiwada ya ƙara da cewa dakatar da jami’an ba zai zama barazana ga tsaron bakin iyakokin ƙasar ba, inda ya ƙara da cewa za su ɗauki matakin zamanantar da ayyukan hukumar domin tabbatar da tsaron ƙasar.

Asali an kafa dakarun haɗin gwiwar ne a ƙarƙashin kulawar ofishin NSA domin yaƙi da fasaƙauri da kwarorowar baƙin haure da wasu manyan laifuka.

hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp