Hukumar da ke kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasa, ta soke lasisin kamfanin jiragen sama na Dana Airlines, daga tsakar daren ranar Laraba, 20 ga watan Yulin 2022.
Dakatarwar ta yi daidai da tanadin sashi 35(2), 3(b) da (4) na dokar hukumar ta 2006, da kuma wani sashe na 1.3.3.3(a)(1) na dokar hukumar zirga-zirgar jiragen sama, ta 2015, suka tanada .
Hukumar kuma ta nemi fasinjoji wadanda su dakatarwar za ta fi shafa, da su fahimci dokar cewa an zartar da ita ne domin kare lafirsu, saboda a cewar hukumar ta fi bayar da muhimmanci kan lafiyar jirage fiye da komai. In ji BBC.