Hukumar shige da fice ta Najeriya ta rasa wasu jami’anta a hanyar Kano zuwa Zariya a ranar Lahadin da ta gabata.
Jami’an wadanda ke kan hanyarsu ta komawa Abuja daga Kano bayan wucewar fareti (POP-out-Parade) a makarantar horas da shige da fice suka yi hatsari.
An tattaro cewa mutane biyu sun mutu bayan hadarin mota.
Hukumar ta tabbatar da faruwar lamarin a shafinta na X na hukuma.
Ta rubuta, “Kyandir ɗinmu suna tashi yayin da zukatanmu suka yi nauyi.”
Jami’in hulda da jama’a na hukumar FRSC reshen jihar Kano Labaran Abdullahi ya bayyana cewa jami’ai biyu sun mutu nan take, yayin da wasu bakwai kuma aka kai asibiti domin kula da lafiyarsu.
A cewarsa, jami’ai tara ne a cikin motar lokacin da hatsarin ya afku.