Hukumar Kula da Jiragen Kasa ta Najeriya ta dakatar da jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna, bayan da wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna ranar Litinin da daddare.
A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na twitter da safiyar nan, ta ce, “saboda wasu dalilai da ba mu shirya musu ba, mun dakatar da jigilar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna. Nan gaba za mu yi muku karin bayani idan akwai”.
Rahotanni daga Najeriya na cewa an sace wasu fasinjoji da ba a bayyana adadinsu ba daga wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna a yammacin ranar Litinin.
Shaidu sun ce, jirgin ya kauce daga kan hanyarsa bayan fashewar wani abu a kan hanyarsa.
Rahotanin sun ce an samu asarar rayuka yayin da wasu da dama suka jikkata.
An kai wa jirgin kasan mai dauke da fasinjoji kusan 1,000, harin ne da misalin karfe 8 na dare.
Fasinjoji da kuma ‘yan uwan wasu fasinjojin sun shaida wa BBC cewa, lamarin ya yi matukar muni kuma har yazu ba a san takamaiman mutanen da lamarin ya shafa ba.
Wani fasinja ya shaida mana cewa bayan jirgin ya tsaya, ‘yan bindiga sun kewaye shi tare da bude wuta.
Mutane sun sunkuya kasa domin samun mafaka kuma daga nan ne maharan suka nufi hanyar jirgin, inda suka harbe fasinja daya a kusa da inda suka yi awon gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba, in ji shi.