Hukumar Alhazai NAHCON, ta ce, za ta nemi hukumomin Saudiyya da su mayar wa alhazan kasar kudin abincinsu a wuraren da ba a ba su abincin ba.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, ta ce shugaban hukumar Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ne ya bayyana hakan a lokacin da ya kai wa alhazan kasar ziyara a Muna.
Mafiya yawan alhazan Najeriya sun yi korafi a kan tsarin da aka bi wajen ciyar da su a aikin Hajjin bana.
Shugaban ya kara da cewa tuni hukumar ta aika da wasika zuwa ga hukumomin Saudiyya domin bayyana korafinta, akan da yadda aka gudanar da tsarin ciyar da alhazai a lokacin aikin Hajjin bana.
Rashin wadataccen abinci na daga cikin kalubalen da alhazan Najeriya suka fuskanta a bana.
Bayan maniyyata akalla 3,000 da ba su samu damar zuwa aikin Hajjin na bana ba. In ji BBC.