fidelitybank

Hukumar Alhazai a Kano ta bayar da wa’adin kwanaki 7 ga maniyata

Date:

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano, ta ce, za ta rufe karbar kudin aikin hajjin 2022 daga masu niyyar zuwa aikin hajji a ranar 12 ga watan Mayu.

Ya ce, za a kawo karshen karɓar kuɗaɗen ne, saboda ayyukan hajjin na kara kusantowa.

Sakataren zartarwa na hukumar, Alhaji Mohammad Abba-Danbatta, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirye-shiryen aikin hajjin 2022 a ranar Alhamis a Kano.

Abba-Danbatta ya bukaci dukkan maniyyatan da su kammala biyan kudin aikin hajjin su cikin kwanaki bakwai.

“Hukumar aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ta kuma bayar da Naira miliyan 2 da digo 5 a matsayin wa’adin tafiyar da aikin na shekarar 2022 sakamakon tashin farashin dala da kuma karin kudaden haraji daga Saudiyya da kamfanin jiragen sama.

“Hukumar tana da akalla mutane 2,500 da suka bayar da wani kaso na kudaden aikin Hajji kuma za su ba da fifiko ga wadanda suka fara saka kudadensu ga hukumar,” inji shi.

Ya shawarci mutanen da suka haura shekaru 65 da su daina yunkurin sauya shekarsu, saboda hukumomin Saudiyya ba za su bari su shiga kasa mai tsarki ba.

nigerianewstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp