Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF, ta kori kociyan kungiyar Salisu Yusuf da Nduka Ugbade.
An kori Yusuf da Ugbade ne saboda munanan rawar da kungiyoyinsu suka yi.
Shugaban NFF Ibrahim Gusau ne ya bayyana sallamar su a wata tattaunawa da yayi da Complete Sports.
“Ayyukan su suna da alaƙa da gasar. Kociyoyin ba su da aikin yi a yanzu, tun da kungiyoyinsu suka kasa tsallakewa,” inji shi.
Kungiyar ta Yusuf ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin Afrika ta U-23, kuma a sakamakon haka, ba za ta kasance cikin gasar kwallon kafa ta Olympics na gaba ba.
Golden Eaglets kuma ta yi waje da gasar cin kofin Afrika na ‘yan kasa da shekaru 17 a zagaye na takwas.
Hakan kuma ya sa Najeriyar da ta lashe gasar sau biyar a duniya ba ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya na gaba.