Ministar kasafin kuɗi ta kasa, Zainab Ahmed, ta ce, Najeriya ba ta talauce ba.
Ta bayyana hakan ne a wurin taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.
Hajiya Zainab ta ce har gobe gwamnatin ƙasar na ci gaba da raba kuɗaɗe daga asusun tarawa da rarraba kuɗaɗe na gwamnati.
Ta ce daga shekarar 2015 zuwa yau gwamnatin tarayya ta bai wa na jihohi kuɗi naira tiriliyan 5.04.
Ta ƙara da cewa har yanzu Najeriyar ba ta gaza wajen biyan basussukan da ake bin ta ba, a ciki da wajen ƙasar.
Ministar ta kuma ce yawan man fetur da ƙasar ke haƙowa na ƙara yawa, inda ta ce a watan Oktoba yawan man ya kai ganga miliyan 1.4 a kowace rana.