Mayaƙan Houthi na Yemen sun yi iƙirarin kai hari kan wani jirgin ruwan Amurka a tekun Bahar Maliya, a wani sabon hari da suka kai kan jiragen jigilar kayayyaki.
Mayaƙan sun kira sunan jirgin da suka kai wa hari da KOI, wanda suka ce Amurka ke sarrafa shi.
Jami’an tsaron tekun sun ce wani jirgi da ke aiki a Kudancin tekun ya bayar da rahoton fashewar wani abu a yankin sai dai babu tabbacin ko jirgin da suke magana a kai ne.
A wani labarin, Amurka ta kai sabbin hare-hare kan jirage marasa matuƙa goma a Yammacin Yemen, wadanda ta ce mayaƙan na shirin kaddamar da hare-hare da su.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, KOI wani jirgin dakon kayayyaki ne da kamfanin Birtaniya Oceonix ke tafiyar da shi.
Kakakin mayakan Houthi, Yahya Sarea ya ce jirgin ya nufi tashar jirgin ruwan yankin Falasdinawa da aka mamaye.