‘Yan tawayen Houthi na ƙasar Yemen sun ce sun kai harin makami mai linzami birnin Eilat na ƙasar Isra’ila a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai wa tashar jiragen ruwa ta birnin Hodeidah ranar Asabar.
Wannan ikirari na zuwa ne bayan sanarwar da sojojin Isra’ila suka yi a baya cewa na’urorin tsaronta na sama sun dakile wani makami mai linzami da aka harba daga kasar Yemen da ya nufi ƙasarta.
Harin da Isra’ila ta kai ranar Asabar ya shafi rumbun ajiyar man fetur da ke birnin Hodeidah, lamarin da ya haddasa mummunar gobaara.
Ma’aikatar lafiya ta Houthi ta ce an kashe mutane shida tare da jikkata 80.
Kungiyar – da ke samun goyon bayan Iran – ta yi barazanar mayar da martani.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana mayar da martani ne kan daruruwan jiragen yakin Yemen marasa matuƙa da makamai masu linzami da ake kai wa yankunanta a ‘yan watannin nan.