An rantsar da Hope Uzodinma a matsayin gwamnan jihar Imo karo na biyu.
Gwamnan ya sha rantsuwane filin wasa na Dan Ayiam da ke Owerri, babban birnin ƙasar.
A jawabinsa na rantsuwar kama aiki, Uzodinma ya yi alkawarin ninƙa ayyuka fiye da wanda ya yi a wa’adin mulkinsa na farko.
Ya gode wa al’ummar jihar bisa goyon baya da suka ba shi har ya sake samun nasara.
Ita ma mataimakiyarsa Lady Chinyere Ekomaru, ta sha rantsuwar kama aiki.
Cikin manyan mutane da suka halarci bikin rantsuwar, akwai Shugaba Bola Tinubu, tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.
Haka ma, ɗumbin mutane daga ciki da wajen jihar ne suka halarci bikin rantsuwar na ranar Litinin.


