Ɗaya daga cikin fitattun jarumai na ƴan fim din Hollywood a kasar Amurka, Bruce Willis mai shekara 67 ya yi ritaya daga sana’arsa ta fitowa daga fina-finai.
A wata sanarwa da iyalansa suka fitar, sun ce, an gano cewa, ya na fama da matsalar magana a sanadiyar matsalar ƙwaƙwalwa.
Willis ya yi fice wanda a ka fi sani da sunan John McClane a fim dinsa da ya yi fice 1988, Die Hard.