Ƙungiyar Hezbollah ta ce ta harba ƙarin wasu rokoki zuwa arewacin Isra’ila a tsakar daren jiya.
Ƙungiyar ta ce ta kai harin a kan rumbun makaman Isra’ila da ke Dishon da Dalton duka a arewacin Isra’ila da manyan rokoki.
Ta ƙara da cewa ta kuma harba wasu rokokin zuwa a kan “matattarar maƙiya” da ke Yir’on, wanda wani yanki ne a arewacin ƙasar da ke kusa da kan iyakar Lebanon.
Tun a farkon dare, Hezbollah ta ce ta kai hari a yammaci, kamar yadda ta bayyana a shafinta na Ingilishi a Instagram.
A ranar Litinin, Hezbollah ta ce ta kai hari a sansanin sojin Isra’ila da ke kusa da Tel Aviv.
Rundunar sojin Isra’ila ta ce Hezbollah ta harba mata rokoki 190 zuwa ƙasarta.