Dakarun ƙungiyar Hezbollah sun bayyana cewa, mayaƙansu sun samu nasarar kai hari da jiragensu biyu marasa matuƙa guda biyu waɗanda suka maƙare da bam a kan barikin Zabdin da ke yankin Shebaa.
Wata sanarwa da Hezboollah ɗin ta fitar ta ce jiragen marasa matuƙa sun kai harin ne a daidai inda aka tsara.
Wannan ne karo na farko da Hezbollah ta yi amfani da irin waɗannan bama-bamai wajen kai hari kan cibiyoyin sojin Isra’ila.
Su kuma dakarun Isra’ila, a wani mataki na mayar da martani, suna harba makaman atilare zuwa kusa da wani gari da ke kan iyakar Lebanon.