fidelitybank

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Date:

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani shiri na musamman domin ɗaukar nauyin aurar da matasa da suka tuba daga ayyukan daba.

Kwamandan rundunar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana hakan ne yayin da sama da matasa 1,000 suka ajiye makaman su, suka kuma yi alƙawarin rungumar zaman lafiya.

A cewarsa, wannan shiri wani ɓangare ne na manufofin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ke nufin inganta rayuwar matasa da kuma ba su wata sabuwar dama ta ci gaba da rayuwa mai kyau.

Sheikh Daurawa ya ja kunnen matasan da suka tuba da su tsare mutuncinsu tare da zama nagari a cikin al’umma. Haka kuma ya yi kira ga sauran da ke cikin irin wannan dabi’a da su yi koyi da abokan su wajen barin laifi domin su ma su more zaman lafiya.

Wannan taro ya gudana ne a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai, Kano, tare da halartar jami’an tsaro da shugabannin al’umma.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...
X whatsapp