fidelitybank

Hisbah ta kama Gandaye 11 a Kano

Date:

Hukumar Hisbah ta kama wasu mutane 11 a ranar Talata waÉ—anda aka ga suna cin abinci a lokacin azumin watan Ramadan a jihar Kano.

Jihar Kano – da ke da mafi rinjayen musulmi – ta kasance mai aiki da dokokin shari’a da tsarin addinin musulunci.

Hukumar ta hisbah kan gudanar da bincike a wuraren cin abinci da kasuwanni duk shekara a cikin watan Ramadan.

Kakakin hukumar, Lawal Fagge ya shaida wa BBC cewa an kama mutum 11, maza 10 da na mace É—aya da ba sa azumi.

“Mun kama mutane 11 a ranar Talata ciki har da wata mata da ke sayar da gyaÉ—a da aka ga tana cin kayanta inda wasu kuma suka sanar da mu,” .

“Sauran mutum 10 maza ne, kuma an kama su a fadin birnin musamman kusa da kasuwannin da ake tafka ta’asa.

Amma ya ce daga bisani an sake waÉ—anda aka kama bayan sun yi rantsuwar cewa ba za su sake shan azumi da gangan ba.

Ya kara da cewa za a ci gaba da gudanar da bincike amma ya ce an keɓe waɗanda ba musulmai ba.

“Ba mu kama waÉ—anda ba musulmai ba saboda wannan bai shafe su ba kuma kawai lokacin da za su iya yin laifi shi ne idan muka gano suna dafa abinci don sayar wa musulmi da ya kamata yana azumi.”

Kimanin shekaru 20 da suka gabata ne aka ɓullo da shari’ar Musulunci domin ta dace da dokokin da ba ruwansu da addini a jihohi 12 na arewacin Najeriya, waɗanda galibinsu Musulmi ne.

Watan Ramadan na da matukar muhimmanci a Musulunci.

daily post

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp