fidelitybank

Hisbah ta baza jami’ai 1,223 tare da hana kiɗan DJ a bikin Sallah

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa, ta yi barazanar cewa, za ta tunkari jama’ar da ke yin rawa, ko shagali, ko kuma yin lalata a lokacin bukukuwan Sallah.

Kwamandan Hisbah a jihar, Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN a Dutse ranar Lahadi.

“Muna amfani da wannan dama wajen fadakar da mazauna garin cewa, mazajen mu za su bi duk wanda ya aikata alfasha da sauran munanan dabi’u irin su Dj dance, Gala, da kuma tallace-tallace da amfani da wasan wuta, wanda aka fi sani da ‘Knock out’. ” NAN ta ruwaito kiwamandan yana gargadin mazauna yankin.

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa, Hisbah, ta yi barazanar cewa za ta tunkari jama’ar da ke yin rawa, ko shagali, ko kuma yin lalata a lokacin bukukuwan Sallah.

Kwamandan Hisbah a jihar Ibrahim Dahiru ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Dutse ranar Lahadi.

“Muna amfani da wannan dama wajen fadakar da mazauna garin cewa mazajen mu za su bi duk wanda ya aikata alfasha da sauran munanan dabi’u irin su Dj dance, Gala, da kuma tallace-tallace da amfani da wasan wuta, wanda aka fi sani da ‘Knock out’. ” NAN ta ruwaito kwamandan yana gargadin mazauna yankin.

Jihar Jigawa dake arewa maso yammacin Najeriya jaha ce da akasarin musulmi. Yayin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya ba da damar ’yancin bin addini da akida, yawancin jihohin Arewa sun kafa hukumar Hisbah don tabbatar da tsauraran akidar Musulunci.

Jami’an Hisbah na bin ‘yan kasuwa da masu shaye-shaye da masu yin lalata da sauran wadanda suke ganin sun saba wa shari’ar Musulunci. Galibin wadanda abin ya shafa talakawa ne kuma ’yan Najeriya masu matsakaicin karfi saboda da kyar suke bin manyan mutane.

A cikin hirarsa ta Lahadi, Dahiru ya kuma ce, hukumar Hisbah a Jigawa ta tura jami’anta akalla 1,223, domin gudanar da bukukuwan Sallah mai zuwa a jihar.
Ya ce jami’an za su hada kai da sauran hukumomin tsaro a jihar, domin samar da isasshen tsaro a lokacin bukukuwan.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp