Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta ce za ta dauki sabbin ma’aikata 3,500 a fadin jihar.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina ne ya bayyana hakan ga manema labarai.
Ya ce, wannan na zuwa ne, bayan sahalewar da hukumar ta samu daga Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a wani mataki na kara inganta ayyukan hukumar.
Ya kuma ce, tsarin daukar sabbin ma’aikatan zai baiwa ‘yan Hisbah na sa kai da ake kira ‘Hisbah Marshal’ fifiko, kana daga bi sani sauran mutane su shigo ciki.
Kaso saba’in cikin dari za su kasance cikin Hisbah Marshal bisa irin kokari da gudunmawa da suke baiwa hukumar Hisbah daga daukar su zuwa yanzu.