Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori daya daga cikin kwamandojin ta saboda hada da yin zagon kasa ga yaki da lalata da zamantakewa a jihar.
Babban kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Daurawa, ya tabbatar wa manema labarai hakan a ranar Talata a Kano, inda ya ce wasu jamiāan guda biyar kuma suna kan bincike.
A cewarsa, “Ma’aikatan da aka kora galibi suna hada baki ne da miyagun abubuwa domin su tafka munanan ayyuka a jihar.”
Daurawa ya kara da cewa ya kuma kori mataimakin Sufeto na Hisbah (DSH) tare da bayyana cewa ana neman sa, inda ya ce duk inda aka same shi a kama shi a gurfanar da shi a gaban kuliya.
Ya ce mataimakin Sufetan da aka kora ya saba hada kai da maāaikatan otal din don kada hukumar Hisbah ta kai farmaki a yayin gudanar da ayyukanta.
Ya kuma yi watsi da rade-radin da wani maāabocin Facebook ke yi na cewa jamiāan sa sun yi wa wasu aski wanda ba dan asalin jihar ba da kwalba bayan sun kai farmaki gidan karuwai a jihar.
Ya kuma bayyana zargin a matsayin na āyan taāadda ne, inda ya ce hukumar Hisbah ta gano wanda ya wallafa faifan bidiyon, kuma za a gayyaci wanda ake zargin domin ya tabbatar da ikirarinsa.


