Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata baɗala a Cibiyar Fasahar Sufuri ta Kasa (NITT) da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Kudu a Jihar Kano.
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Mujahid Aminudeen, ya ce mutane — maza 27 da mata 35, “A ranar Lahadi, jami’anmu tare da haɗin gwiwar NDLEA suka su su 62 a cibiyar horarwa ta NITT da ke Dawakin Kudu, bayan samun bayanan sirri daga wasu masu kishin ƙasa.”
Ya ce mutanen sun yi amfani da saukar ruwan sama da ake samu lokaci-lokaci a yankin don aikata baɗala.“Muna amfani da wannan dama don gargaɗi ga matasa masu aikata abubuwan batsa da su daina, ko su fuskanci hukuncin doka. Hisbah ba za ta zauna ba tare da daukar mataki kan masu karya dokar Shari’a ba,” in ji Mujahid Aminudeen.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoto kan duk wani abu da ya saba wa dokar Shari’a a jihar.
Aminudeen ya ƙara da cewa hukumar ta kai wani samame makamancin haka a Gadar Tamburawa, inda aka kama wasu mutane kan laifuka makamanta da haka.
Ya ce duk waɗanda aka kama za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.