Hukumar Hisbah ta jihar Kano, ta kama wasu matasa ‘yan daudu 19 da suka halarci daurin auren abokansu.
Kakakin hukumar, Malam Lawan Ibrahim ya bayyana hakan a ranar Talata, cewa matasan sun hallara ne domin shaida daurin auren wasu da ake zargin ‘yan luwadi ne Abba da Mujahid.
An kama shi ne bayan da wani ya gaya wa hukumar game da auren jinsi É—aya.
“Jami’an mu da ke shedikwatar hukumar Hisbah, Sharada Kano, sun isa wurin kafin a fara daurin auren. Injishi.