Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama kwalaben barasa 8,600 a cikin wata mota da ta zo jihar daga Kaduna.
Jami’in hukumar mai kula da kayan maye, Idris Ibrahim, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a karshen mako, ya ce an kama barasa a ranar Alhamis din da ta gabata a kauyen Kwanar Dangora, da ke kan hanyar Kano zuwa Kaduna.
A cewarsa, jami’an hukumar sun yi ta bin diddigin motar daga Kaduna har ta shigo cikin yankin Kano.
“Mun tsayar da motar a kauyen Kwanar Dangora kuma direban ya yi yunkurin tserewa amma jami’an mu sun kama shi.
by TaboolaSponsored Links Kuna Iya So
Har zuwa Bonus 200,000!
Betano
“Kun san haram ne sayar da giya a jihar Kano. Don haka za mu gurfanar da direban a gaban kuliya bayan mun kai maganarsa,” inji shi.
Ibrahim ya ci gaba da cewa, tawagar Hisbah da ke kula da ayyukan sa maye a hukumar tana jiran karin umarni daga hukumar Hisbah.
Kazalika ta kama wasu mata 15 da laifin karuwanci yayin gudanar da ayyuka a sassa daban daban na cikin birnin Kano.
An kama matan da ake zargi da aikata karuwanci a Hotoro Tishama, Kogin Bakin Verd Sabon Gari, titin Miyangu, titin Hadejia da kuma tsoffin wuraren ajiye motoci na Zoo Road.
Mataimakin babban kwamandan hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, wanda ya tabbatar da kamen, ya ce an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin karuwai sau da yawa, kuma an gurfanar da su a gaban kotu, amma har yanzu suna gudanar da wannan sana’ar ta haramtacciyar hanya.
“Abin takaici ne yadda wasu daga cikin wadannan matan suka bar jihohinsu da kasashensu suka zo Kano inda suke yin karuwanci da wasu munanan dabi’u.
“Suna yawo a kan titunan Kano suna yin abubuwa iri-iri. Muna kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahoton irin wadannan ayyuka domin mu tsaftace jihar,” ya kara da cewa.