Hukumar Hisba ta jihar Kano ta sanar da kama wasu matasa waɗanda ba sa azumi, da waɗanda suka yi aski banza.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin kwamanda-janar na hukumar, Mujahiddeen Abubakar, inda ya ce sun kama matasan ne a lokacin da suke sintiri a sassa daban-daban na Kano.
Haka kuma ya ce sun kama wasu matasa guda 60 da suka yi “askin banza” waɗanda a cewarsa ya saɓa da addinin musulunci da al’adun mutanen yankin.
A wani ɓangaren kuma, ya ce hukumar ta kama wani mai Adaidaita wanda suke zargi da haɗa fasinjoji maza da mata.