fidelitybank

Hisba ta gargadi masu kidan DJ yayin bikin aure a Kano

Date:

Darakta Janar na hukumar Hisbah ta jihar Kano, Abba Sa’id Sufi ya ce hukumar shawarci maza masu kunna kiɗa a gidajen biki da su daian cuɗanya maza da mata a wuraren taruwar bukuwa a faɗin jihar.

Hakan ya ci karo da wasu rahotonni da ke cewa hukumar ta haramta wa maza masu sana’ar DJn halartar bukukuwan mata a faɗin jihar.

Abba Sa’id Sufi ya shaida wa BBC cewa shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka, yayin wani taro da wakilan ƙungiyar masu DJn a jihar inda ya ce matakin ya zama dole a ƙoƙarin da hukumar ke yi na daƙile cuɗanya tsakanin mata da maza a wuraren taruka.

Shugaban na Hisba ya ce ”a matsayin jihar nan ta musulunci, ba za mu bari a dinga cuɗanya tsakanin mata da maza ba a wurin taro. Saboda hakan zai kawo ƙaruwa da kuma yaɗuwar baɗala”.

Ya ƙara da cewa a baya an yi wani taron da masu wuraren biki a jihar domin a wayar musu da kai kan dokokin da suka jiɓanci tafiyar da sana’artasu.

Jagoran wakilan ƙungiyar masu DJ, Ibrahim Farawa wanda aka fi sani da DJ Farawa ya jinjina wa Hukumar kan gayyatarsu da kuma ba su shawarwari kan sabbin tsare-tsare da hukumar ta fitar don lura da al’amuran sana’ar tasu waɗanda suka haɗa da kiyaye lokutan sallah da kuma buƙatar hana cuɗanya tsakanin mata da maza yayin taruka.

DJ Farawa ya yi ƙira ga dukkan masu DJ da ke jihar da su bi dokokin da hukumar ta gabatar domin guje wa aikata laifi.

Sannan ya ƙara kira ga dukkan sana’ar da ke jihar da su yi rijista ƙarƙashin ƙungiyar domin amfana da tsare-tsaren da aka fitar.

Ya kuma gargaɗi waɗanda suka ƙi yin hakan da cewa ƙungiyar ba za ta kare duk wanda aka kama da laifin take dokokin Hisbah ba.

national news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp