Hukumar Hisba ta jihar Kano, ta fasa kwalaben Giya masu tarin yawa da kudin su kai sama da Naira miliyan 100.
Babban kwamandan hukumar, Haroon Muhammad Sani Ibn Sina ne ya jagoranci fasa kwalaben Giyar a yunkurin hukumar da aiki da kyakykyawa da hani da mummuna.
A na dai gudanar da aikin fasa giyar ne a kauyen Kalebawa da ke da nisan kilomita 12 daga shalkwatar karamar hukumar Dawakin Tofa.