fidelitybank

Hisba ta fara kamen mata masu talla a titunan Kano

Date:

Hukumar Hisba a Kano, ta fara shirin kama matan da su ke talla a kan titunan jihar.

Kafar yada labaran Radio Najeriya ta rawaito, mataimakiyar mukaddashin kwamanda mai kula da harkokin mata, Malama Ummulkulsum Kasim ce, ta yi wannan bayanin, bayan kama wasu mata a titunan karamar hukumar Kumbotso.

Malama Ummulkulsum ta ce, yawancin matan da ke talla akan tituna da daddare ‘yan mata ne da ke saida gyara da goro, da rogo, ko kayan lambu da sauransu.

Ta ce, yawancin ‘yan tallan an gano su a tashoshin mota, da wurin makanikai abin takaicin kuma da daddare.

Malama Ummulkulsum ta ce, ”hakkin iyaye ne killace ‘ya’yansu da tabbar da ba su tarbiyya da ilimi, da kare su daga aikata ba daidai ba. Kuma addinin musulunci ya tabbatar da hakan, bai kamata a bar ‘ya’ya mata da na yawo kara zube da sunan talla ba.”

Radio Nigeria ta rawaito kwanakin da suka gabata hukumar Hisba a jihar Kanon ta yi nasarar kama wasu matasa 19 kan zargin halartar auren jinsi a Kano, ko da ya ke Amarya da Angon sun tsere har yanzu ba a san inda suka buya ba.

sun newspaper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp