fidelitybank

Hisba ta cafke Bokon da ake zargi da kawalci da baɗala a Kano

Date:

Hukumar Hisbah ta jahar Kano, ta kama Wani mutum Mai suna, Umar Sokoto, Dan Shekaru 50, bisa zarginsa da harkar Bokanci da kuma yada baɗala shida wani matashi wanda suke harkar kawalci.

Hukumar ta cafke mutanen ne biyo bayan korafe-korafen da al’ummar Sheka layin shugaban karamar hukumar Kumbotso, suka yi kan zargin Bokanci da Kawalcin da ake yi a yankin.

Jami’an sun bayyana cewa, an samu mace da namiji a gidan mutumin, wanda yanzu haka ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Haka zalika an samu wasu kayayyaki , a gidan da ake zargin ana yin amfani da su.

Sai dai mutanen sun musanta Zargin bokanci, amma sunce hada Mata da Maza waje guda ba daidai ba ne kuma ba za su kara ba.

Umar Sokoto ya ce baya yin Bokanci Amma Yana bayar da maganin Neman farin Jini ga mata , kuma yau shekarun sa biyar bai taba samun matsala da kowa ba, Inda yanzu haka ya ce, zai koma gida Sokoto bayan an Yi masa wa’azi kuma ya daina.

the nation newspaper 
today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp