fidelitybank

Hisba ta cafke ƴan Mata da Maza ma su yawon dare a Kano

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane 10 da suka hada da mata takwas da maza biyu, bisa zarginsu da yawon ddare a sassa daban-daban na jihar.

An yi kamen ne a wani bangare na yakin da ake yi na “Operation Clean Up” da nufin inganta zaman lafiyar jama’a da kuma kula da tsaftar kawar da baɗala.

Da yake zantawa da manema labarai, mukaddashin kwamandan Hisbah, Aminudden Mujahiddeen, ya bayyana cewa an kama mutanen ne a tashar mota ta Kofar Ruwa, titin filin jirgin sama, Sabon Gari, da sauran wurare.

Ya bayyana cewa wasu daga cikin wadanda aka kama ana zarginsu da safarar miyagun kwayoyi da kuma nemansu. “Wasu ma ba ’yan Kano ba ne. Hasali ma daya daga cikin matan ba ‘yar Najeriya ba ce,” Mujahiddeen ya bayyana.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kuma za a dauki matakin da ya dace a wani bangare na kokarin tabbatar da doka da oda a jihar.

legit news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp