fidelitybank

Hisba na neman su Murja ruwa a jallo a Kano

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da sanarwar neman wasu shahararrun masu amfani da shafin Tiktok guda shida saboda furta kalaman batsa cikin wasu bidiyo da suka yi, lamarin da ya ci karo da dokar tabbatar da tarbiyya.

Shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida wa BBC cewa cikin masu amfani da shafin da ake nema akwai Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gfresh sai Sadiya Haruna da Ashiru Idris da aka fi sani da Maiwushirya da Ummee Shakira da Murja Ibrahim Kunya da kuma Hassan Makeup.

A cewar Sheikh Daurawa, suna cigiyar mutanen ne bayan É“ullar wani bidiyo da a ciki suke furta kalaman da ba su dace ba wanda kuma ya ci karo da alkawarin da suka yi lokacin da aka kama su a karon farko domin yi musu wa’azi.

Ya ce babban burin Hisbah shi ne ta ga an gyara kura-kurai tun da “ba so muke mu ci gaba da gayyato mutanen ba, watakila hakan zai sa su ji cewa ba su kyauta ba tun da an yi yarjejeniya da su, sun yi mana alkawari za su gyara [amma hakan ba ta faru ba].”

Sheikh Daurawa ya ce kasancewar wannan ne karo na biyu da suke saba dokar ta tarbiyya, ko da sun bayyana a gaban Hisbah, za su sake jan hankalinsu a kan yin irin wadannan dabi’u tare da tabbatar da cewa sun rubuta alkawarin riko da yarjejeniyar da aka yi da su.

Ya ce sai mutum ya taka doka sau uku sannan ake gurfanar da shi a gaban kotu.

“Ba kotu za mu kai su ba yanzu, ai yarjejeniya sau uku ake yi, idan suka zo, za mu ce musu ya muka yi yarjejeniya da ku, bayan kun gaya mana ba za ku sake ba kuma kuka sake, sai mu ji uzirinsu.” in ji Sheikh Daurawa.

Shugaban hukumar ta Hisbah ya ce a baya, sun tattauna da jami’ai daga ofishin Tiktok da ke Legas inda kuma suka ce idan aka samu masu amfani da Tiktok da yake saba doka ko jayo tashin hankali ko É“ata addini “idan muka rubuta muka kai musu, suka bayar da rahoto, za a iya toshe [shafinsa].”

“Wannan ma ya fi yi wa dan Tiktok zafi, ka sa a goge shafinsa domin wani ya tara mabiya da yawa, idan ya ji za a rufe shafinsa saboda gwamnati ta shigo, kuma doka ya karya.” in ji Daurawa.

A shekarar da ta gabata ne hukumar ta Hisbah ta gana da yan Tiktok a Kano domin tattaunawa da su game da yadda za a tabbatar da kyawawan dabi’u tare da kawar da fitsara a shafin.

latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp