Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa, ta kona barasa fiye da 5,550 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 3.2.
Kwamandan Hisbah na jihar, Ibrahim Dahiru, ya bayyana haka bayan lalata barasa a karamar hukumar Kazaure.
Ya ce, an kama barasa ne a ayyukan rundunar da ke ci gaba da yi a jihar.
“A cikin makonni mun kama barasa da ya kai kwalabe 5,550 da gwangwani da aka ce sun kai Naira miliyan 3.2,” inji shi.


