Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya gargadin ƙungiyar Hezbollah mai ƙarfin soji a Lebanon, game da ƙaddamar da hari kan Isra’ila a karo na biyu.
“Zai zama babban kuskure da ƙungiyar za ta yi a rayuwarta, idan ta kawo mana hari”, kamar yadda Netanyahu ya shaida wa dakarun Isra’ila da ke kusa da kan iyakar Lebanon.
Ya ce hakan zai sa Isra’ila ta ƙaddamar da munanan hare-hare da za su “wargaza” Lebanon.
Isra’ila da Amurka sun gargaɗi ƙasar Iran – da ke goyon bayan Hezbollah, wadda Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashen yamma suka ayyana a matsayin ‘ƙungiyar ta’adanci’ – kan buɗe wani sabon yaƙi a kan iyakar arewacin Isra’ila.