fidelitybank

Hezbollah ta yi lugudan wuta a kan Isra’ila

Date:

Da safiyar ranar Asabar ne ƙungiyar Hezbollah a Lebanon ta ce ta harba makamai masu linzami zuwa ɓangaren da ‘cibiyar kula da sararin samaniyar Isra’ila take’, a wani abu da ta bayyana da ramuwar gayya kan kisan da aka yi wa mataimakin shugaban kungiyar Hamas a Beirut, Saleh Al-Arouri.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce cikin wata sanarwa da Hezbolla ta fitar ta ce ”a wani martani na kisan Sheikh Saleh Al-Arouri da wasu ‘yan uwansa a kudancin birnin Beirut, ƙungiyar ta kaddamar da hare-haren makamai masu linzami aƙalla 62 kan cibiyar kula da sararin samaninar Isra’ila ta Meron.

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyar ta samu tabbacin cewa makaman sun shafi cibiyar.

Cibiyar Meron – wadda ke kan tsaunin Jarmaq da ke arewacin ƙasar – na ɗaya daga cikin cibiyoyi biyu da Isra’ila ke amfani da su wajen lura tare da kare sararin samaniyarta.

AFP ya ce sojojin Isra’ila sun bayyana kakkaɓo hare-haren makamai masu linzami kimanin 40 da aka harbo daga ƙasar Lebanon a ranar Asabar da safe a ɓangaren cibiyar Meron.

An yi ta jin ƙarar na’urar ankararwa a biranen da ke arewacin Isra’ila da ɓangaren tuddan Gola.

A ranar Talatar da ta gabata ne wani hari da aka yi amanna na jirgi maras matuƙi ne a birnin Beirut ya yi sanadin kisan Saleh Al-Arouri.

Inda hukumomin Lebanon da ƙungiyar Hamas da Amurka suka zargi Isra’ila ta kai harin, to sai dai Isra’ila ba ta ɗauki alhakin harin ba.

vangurd 
news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp