Ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta tabbatar da kisan jagoranta Hassan Nasarallah.
Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Telegram, ta ce ”za ta ci gaba da yaƙi da Isra’ila da goyon bayan Gaza da Falasɗinawa tare da kare Lebanon da mutanenta”.
Tun ɗazu ne dai Isra’ila ta fitar da sanarwar kisan jagoran ƙungiyar, a wani hari da jirgin yaƙinta ya kai tsakiyar shalkwatar Hezbollah, da ta ce yana ƙarƙashin ƙasa a ƙasan wani gida da ke unguwar Dahieh a birnin Beirut. In ji BBC.


