Rundunar sojojin Isra’ila ta tabbatar da saukar jerin gwanon rokoki a arewacin ƙasar da mayaƙan Hezbollah suka harba.
Rundunar ba ta yi bayani ba dangane da illar da rokokin suka yi.
Sai dai rundunar ta ce an kunna alamun da ke ankarar da jama’a idan an samu hari a yankin arewacin.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Isra’ilar ta ce ta ƙaddamar da wasu hare-hare a kan ɗaruruwan rokokin kungiyar Hezbollah.